Albarkacin ranan tunawa da mazajen fama: An saki fursunoni 244 da ake zargin suna da alaka da Boko Haram

Albarkacin ranan tunawa da mazajen fama: An saki fursunoni 244 da ake zargin suna da alaka da Boko Haram

- An saki yan Boko Haram 244 a jihar Borno

- Sun samu yanci bayan bincike mai zurfin da aka gudanar kuma aka wanke su

A yau Litinin, 15 ga watan janairu, 2018 hukumar sojin Najeriya ta saki mutane 244 da ake zargi da zama yan Boko Haram a jihar Borno.

Kwamandan rundunar Operation LAFIYA DOLE, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya sanar da sakinsu ne a taron tunawa da mazajen faman da suka rasa rayukansu a faggen fama a makabartan barikin sojin Maimalari Cantonement da ke Maiduguri, jihar Borno.

Albarkacin ranan tunawa da mazajen fama: An saki fursunonin ake zargi da Boko Haram 244

Albarkacin ranan tunawa da mazajen fama: An saki fursunonin ake zargi da Boko Haram 244

Yace: “ Bayan binciken wadanda ake zargin, hukumar soji na farin cikin mikasu ga gwamnatin jihar Borno,”.

KU KARANTA: Duk wanda aka tura jihar Benuwe ko Taraba ya tafi sansanin horon jihar Kogi - NYSC

Daga baya gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya yi magana da fursunoni a filin paretin da aka gudanar da taron.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel