Hukumar SUBEB a Kaduna za ta kashe N337.19m domin bayar da horo ga malaman makarantun jihar

Hukumar SUBEB a Kaduna za ta kashe N337.19m domin bayar da horo ga malaman makarantun jihar

- Hukumar SUBEB a jihar Kaduna za ta kashe miliyan N337.19 domin bayar da horo ga malaman makarantun jihar

- Kwana nan jihar Kaduna ta kori malaman makarantun firamare 22,000

- Horon zai shafi malamai a matakai daban-daban

Duk da rikici da ake ta gwabzawa tsakanin kungiyoyin kwadago da na ma'aikata a bangare guda da kuma gwamnatin jihar Kaduna a daya bangaren, sakamakon korar malaman makarantun firamare 22,000 da gwamnatin jihar ta yi, hukumar kula da ilimi a jihar Kaduna (SUBEB) ta ce za ta kashe miliyan N337.19 domin bayar da horo ga malaman makarantun jihar a shekarar 2018.

Hukumar SUBEB a Kaduna za ta kashe N337.19m domin bayar da horo ga malaman makarantun jihar

Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa'i

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar ya tabbatar da hakan daga kwafin kasafin kudin jihar na shekarar nan da ya samu daga ma'aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar.

Za'a bayar da horon ne ga malaman makarantu a matakai daban-daban da suka hada har da malaman makarantun almajirai 200. Malaman makarantun gwamnati 1,200 ne zasu ci moriyar horon.

DUBA WANNAN: Takardar sallama daga aiki ta kusa hallaka masinja a jihar Kaduna

Horon zai shafi bangarori da dama da suka hada da; dabarun karatu, dabarun shugabanci, tsara jadawalin koyarwa, ilimin bibiyar kwazon dalibai, da sauran su.

NAN ta rawaito cewar biliyan N6.93 ne kasafin hukumar SUBEB na wannan shekarar a jihar Kaduna, N6.75 za'a kashe domin manyan aiyuka a fadin makarantun jihar, adadin da ya ninka wanda aka bawa jihar a kasafin kudin bara, 3.36.

Hukumar zata kashe biliyan N3.53 domin gina ajuzuwa, ofisoshi, da kuma bandakai a makarantun firamare, biliyan N1.89 za'a kashe su domin gina ajuzuwa da dakunan bincike a kananan makarantun sakandire.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel