Yan sanda sun kama mutane 59 kan rikicin Wadata a Benue

Yan sanda sun kama mutane 59 kan rikicin Wadata a Benue

- An kama mutane 59 dake da alaka da rikice-rikice da suka afku a wasu yankuna na Makurdi

- Mutane da dama sun ji rauni sannan kuma anyi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira a lokacin rikicin

- Za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu da zaran an kammala bincike, a cewar yan sandan

Rundunar yan sandan jihar Benue ta ce ta kama mutane 59 dake da nasaba da rikice-rikicen da ya afku kwanan nan a wasu yankuna na Makurdi, jihar Benue.

Mutane da dama sun ji rauni sannan kuma anyi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira a lokacin rikicin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Moses Yamu, ya bayyana hakan a wani hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Litinin a Makurdi.

Ya bayyana cewa tuni rundunar ta karo jami’an tsaro a guraren da abun ya shafa domin a dawo da zaman lafiya da kuma doka da kuma gano abun da ya wanzar da rikicin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)

Ya kuma sanar da cewa Za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu da zaran an kammala bincike. Sannan ya ja kunnen mazauna garin Makurdi da su guje ma tashe-tashen hankula.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel