Fadar shugaban kasa ta mayar wa Fasto Tunde Bakare martani akan kakkausar suka da ya yiwa gwamnatin Buhari

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Fasto Tunde Bakare martani akan kakkausar suka da ya yiwa gwamnatin Buhari

- Fasto Tunde Bakare ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen cika alkawrran da ta yiwa yan Najeriya

- Femi Adesina ya ce gwamnatin Buhari tana kan gyara kuma zata cika alkwarran da ta yiwa yan Najeriya

Fadar shugaban kasa ta mayar wa shugaban cocin Pentecostal, Fasto Tunde Bakare, martani akan kakkausar sukar da ya yiwa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na cewa ta kasa cika alkawarran da ya yiwa yan Najeriya.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya karyata wannan zargi inda ya ce, gwamnati Buhari tana kan hanyar gyara.

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Fasto Tunde Bakare martani akan kakkausar suka da ya yiwa gwamnatin Buhari

Fadar shugaban kasa ta mayar wa Fasto Tunde Bakare martani akan kakkausar suka da ya yiwa gwamnatin Buhari

Femi Adesina yace, gwamantin Buhari ta na kan hanyar gyara kuma zata cika duka alkwarran da ta yi wa yan Najeriya.

KU KARANTA : Dala miliyan $44m ba su bace daga asusun hukumar NIA ba – Jami’in hukumar NIA

Femi Adesina ya bayyana haka ne wata hirar da yayi a gidan Talabijin na Channels TV a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu, 2018.

Wannan martanin ya zo ne sa’o’i kadan bayan, Fasto Tunde Bakare, yayi kakkausar sukar ga gwamnatin Buhari a lokacin da yake wa’azi a ciki cocin sa dake Legas, inda yace gwamnatin Buhari ta gaza a fannin tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel