Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Gwamna Samuel Ortom da kuma dattawan jihar Benue akan kashe-kashen makiyaya a jihar.

Jihar Benue ta shiga halin juyayi kan kashe-kashen da ake ta fama da shi a jihar sannan kuma a baya shugaban kasa Buhari ya tura Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris jihar domin ya magance mawuyacin halin da ake ciki.

Shugaban kasar ya gana da dattawan Benue a cikin fadar shugaban kasa, a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu domin tattaunawa kan yadda za a cimma zaman lafiya.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci

Wadanda suka halarci ganawan sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tsohon gwamna George Akume, sarkin Tiv, farfesa James Ayatse; Sanata Barnabas Gemade, tsohon ministan shari’a Michael Aondoakaa, Sanata Joseph Wayas; da kuma kakakin majalisar dokoki na jihar Terkimbir Kyamb.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta aika sammaci ga jakadan Amurka kan furucin Trump na cewa yan Afrika wulakantattu ne

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci (bidiyo)

Shugaba Buhari, Gwamna Ortom da dattawan Benue na cikin ganawa mai muhimmanci

Har ila yau ministan tsaro Mansur Dan-Ali; ministan noma, Audu Ogbegh; ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazzau da sauran jami’an gwamnati sun halarci ganawan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel