Siyasa: Buhari ba zai cece ku a shekara ta 2019 ba, PDP ta gargadi gwamnonin APC

Siyasa: Buhari ba zai cece ku a shekara ta 2019 ba, PDP ta gargadi gwamnonin APC

- PDP ta caccaki gwamnonin APC cewa Buhari ba zai cece su ba a zaben 2019

- Jam’iyyar ta ce gwamnonin APC suna tururuwa zuwa Abuja don saduwa da shugaba Buhari a kan zabe ta shekarar 2019

- Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce APC ta firgita saboda 'yan Najeriya sun sabunta sha'awarsu a PDP

Babban jam’iyyar adawa ta PDP ta ce shugaba Muhammadu Buhari ba zai ceci gwamnonin jam'iyya mai mulki ta APC ba daga shan kashi a shekarar 2019.

Jam’iyyar ta caccaki gwamnonin APC cewa suna tururuwa zuwa Abuja don saduwa da shugaba Buhari domin samun sauƙi a zaben shekara ta 2019 saboda rashin aikinsu.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, a cikin wata sanarwa da aka bayar a Abuja, sakataren hulda da jama’a na jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya kuma kalubalanci APC da ta gaggauta gwada shahararta a tsakanin 'yan Najeriya ta hanyar gudanar da zaben kananan hukumimin a jihohin da suke mulki.

Siyasa: Buhari ba zai cece ku a shekara ta 2019 ba, PDP ta gargadi gwamnonin APC

Shugaba Muhammadu Buhari, tare da wasu gwamnonin APC

"APC ta san cewa ba za ta iya fuskanci 'yan Najeriya fiye da miliyan takwas ba, wadanda suka rasa ayyukansu ta hanyar manufofi mara kyau. Sun san cewa hukunci yana jiran su daga dubban ma'aikata wadanda aka kori a jihohin da gwamnonin APC ke mulki, musamman Kogi da Kaduna”.

KU KARANTA: Goodluck Jonathan ya aika gagarumin sako ga rundunar sojin Najeriya a ranar ta

Mai magana da yawun PDP ya ce, “APC ta firgita saboda 'yan Najeriya sun sabunta sha'awarsu a PDP a matsayin jam’iyyar mai mutanen kirki na gaskiya".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel