Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta aika sammaci ga jakadan Amurka kan furucin Trump na cewa yan Afrika wulakantattu ne

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta aika sammaci ga jakadan Amurka kan furucin Trump na cewa yan Afrika wulakantattu ne

Gwamnatin tarayya ta aika sammaci ga jakadan kasar Amurka a Najeriya, Stuart Symington, kan kalamun wulakanci da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi.

Shugaba Trump ya caccaki yan ci rani, inda ya bayyana cewa sun fito daga wulakantattun kasashe, furucin da ya fusata kasashe da dama da abun ya shafa sannan kuma ya janyo suka mai tsanani daga kungiyar kasashen Afrika da sauransu.

Ana sa ran Symington zai gana min istan harkokin waje, Geoffrey Onyeama a yau.

Idan zaku tuna a baya Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi wasu kalaman wulakanci kan yan ci rani da suka fito daga kasashen Haiti, El Salvador da kuma Afirka.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Trump ya tambayi majalisar dokoki kan dalilin da ya sa mutanen wadannan kasashe na Afirka sunka shigo kasarsu.

KU KARANTA KUMA: Lokaci ya yi da ya kamata ayi ma Najeriya garambawul – Shugaban CAN ga Buhari

Ya ce: "Me ya sa wadannan mutanen da suka fito daga wulakantattun kasashe suka shigo nan?" kamar yadda kafafen watsa labaran Amurka suka trahoto.

Wadannan kalamai, wadanda ya yi a lokacin da suke tattaunawa kan shige-da-fice, ya yi su ne kan 'yan kasashen Afirka da Haiti da kuma El Salvador.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel