Lokaci ya yi da ya kamata ayi ma Najeriya garambawul – Shugaban CAN ga Buhari

Lokaci ya yi da ya kamata ayi ma Najeriya garambawul – Shugaban CAN ga Buhari

Shugaban kungiyar kiristoci Najeriya, Rev. Dr. Samson Olasupo Ayokunle, ya bayyana ra’ayinsa na sake fasalin kasar.

Ya ce dole a sake kayyade rabuwar kasa da kuma coci. Yayinda baza a yarda kasa ta kula da coci ba, dole cocin tayi tasiri kan kasar ta hanyar kiristoci dake kan mulki.

Ayokunle, wanda ya kasance shugaban kungiyar Baftisma na kasa, ya bayyana haka, a babban birnin tarayya Abuja a taron shakatawa na ma’aikatan kasa. Ya cigaba da cewa bayan shekaru 57 da samun yanci, kasar ta isa a sake mata fasali kuma ba tare da tsoro ko nuna kauna ba.

Lokaci ya yi da ya kamata ayi ma Najeriya garambawul – Shugaban CAN ga Buhari

Lokaci ya yi da ya kamata ayi ma Najeriya garambawul – Shugaban CAN ga Buhari

Shugaban kungiyar CAN din ya yi kira ga kiristoci da su rungumi siyasa, idan suna son su taka rawa a fagen siyasa. Yayi nuni cewa: “Domin isa kan matsayin mulki, akwai bukatar ayi zabe, musamman a tsarin damokardiyya irin namu. Dole mu shiga siyasa.”

Shugaban kungiyar CAN din yayi addu’a don zaman lafiya kan kashe-kashen al’ummar jihohin Benue da na Taraba da makiyaya suka yi. Ya roki Allah da ya jajenta sauran al’umman ya kuma warkar da masu jinya.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani gagarumin aiki a makarantar sojin sama na Uyo (hotuna)

Har ila yau ya kalubalance gwamnati da hukumomin tsaro, inda yake cewa: “Da an kauce ma zubda jini da ace shuwagabannin siyasa da shuwagabannin hukumomin tsaro sun kasance masu riko ga ayyukansu.

"Wannan ne dalilin da yasa kungiyar CAN ta cigaba da kira garesu. Abunda ke faruwa a yankin arewa ta tsakiyar kasa abun kunya ne. mugunta ne da fasikanci. Ya kamata mu tsayar da al’amarin kafin mu fada cikin yakin basasa wanda ba a bukata.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel