Gwamnatin tarayya za ta raba jarin biliyan N10 ga matasa miliyan daya a karkashin sabon tsarin NEPRO

Gwamnatin tarayya za ta raba jarin biliyan N10 ga matasa miliyan daya a karkashin sabon tsarin NEPRO

- Gwamnatin ta ce za ta raba jarin biliyan N10 ga matasa miliyan daya

- Za'a bayar da jarin ne domin bunkasa samar da kwai

- Matasa 18,000 zasu amfana da sabon shirin NEPRO a jihar Ondo

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin raba jarin biliyan N10 ga matasa miliyan daya a karkashin sabon shirin gwamnati na samar da kwai (NEPRO).

Ministan harkokin Noma da raya karkara, Audu Ogbeh, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a jihar Ondo. Ya ce babban kasa (CBN) ne zai samar da kudaden da bankin harkokin noma (BoA) zai raba ga matasan a kan tsari mai rangwame. Za'a fara kaddamar da shirin a jihohin Najeriya guda shida; Abiya, Kuros Riba, Ondo, Kebbi, Kogi, da Ondo.

Gwamnatin tarayya za ta raba jarin biliyan N10 ga matasa miliyan daya a karkashin sabon tsarin NEPRO

Ministan Harkokin Noma da Raya karkara

Ministan ya ce kowanne manomi zai samu rancen miliyan 4.2 da zai biya cikin watanni 30. Ya ce za'a bawa matasan tsabar kudi miliyan N1.68 yayin da za'a yi amfani da naira miliyan N2.8 wajen saya masu kadaran da zasu yi amfani da su wajen sana'ar su.

Ogbeh ya bayyana halin karancin aikin yi da matasa ke ciki da wulakanta noma da aka yi a Najeriya da kuma dogaro kacokan a kan man fetur.

DUBA WANNA: Nasarorin da Buhari ya samu ne suka jazawa mulkin jam'iyyar PDP na shekaru 16 bakinjini - Oyegun

Ministan ya bayyana kaddamar da shirin ne a garin Aaye, jihar Ondo, dake kudu maso-yammacin Najeriya.

A jawabinsa, gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na hada gwuiwa da ma'aikatar harkokin noma ta tarayya domin samar da aiki ga matasa.

Akeredolu ya kara haske a kan kokarin gwamnatin jihar na bunkasa harkar noma, yana mai bayyana kammala shirin fara gina wani katafaren kamafanin kyankyasar kwai na naira biliyan N42 da za'a fara saka tubalinsa ranar 22 ga watan Fabrairu, 2018, kazalika ya bayyana cewar gwamnatin jihar na daf da kammala ginin wani kamfanin alewa da ya gada daga gwamnatin da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel