Goodluck Jonathan ya aika gagarumin sako ga rundunar sojin Najeriya a ranar ta

Goodluck Jonathan ya aika gagarumin sako ga rundunar sojin Najeriya a ranar ta

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya aika sakon jinjina ga rundunar sojin Najeriya

- Ya yaba masu bisa irin rawar ganin da suke takawa wajen ganin sun tsare rayuka da dukiyoyin al’umman kasar daga hannun yan ta’adda

- Ya musu fatan alkhairi tare da addu’an Allah ya albarkace su

A ranar Litinin, 15 ga watan Janairu 2018 wanda ya yi daidai da ranar tunawa da rundunar sojin kasar, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya aika sako na musamman ga rundunar tsaron kasar.

Jonathan ya yaba masu bisa irin rawar ganin da suke takawa wajen ganin sun tsare rayuka da dukiyoyin al’umman kasar daga hannun yan ta’adda. A cewarsa sune suka zamo Katanga tsakanin al’umman kasar da mutuwa.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce da shi da iyalansa suna yi ma hukumomin tsaron fatan alkhairi da kuma addu’an Allah ya albarkaci rayuwarsu.

Goodluck Jonathan ya aika gagarumin sako ga rundunar sojin Najeriya a ranar ta

Goodluck Jonathan ya aika gagarumin sako ga rundunar sojin Najeriya a ranar ta

Daga karshe ya yi kira ga al’umman kasar da su ware lokaci domin taya rundunar tsaro raya wannan rana mai matukar muhimmanci a garesu.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai halarci taron ranar tunawa da hukumomin tsaro na 2018

Ga yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook:

“Hukumomin tsaronmu sune ginshin da suka yi mana Katanga da mutuwa da kuma halaka a hannun yan ta’adda dfa sauran abubuwan dake wa tsaron kasarmu baraza. Da dama daga cikin dakarunsu sun yi gagarumin sadaukarwa sannan kuma dani da iyalaina muna gode ma hukumomin tsaron Najeriya bisa sadaukarwarsu da jajircewarsu akan kasar. A wannan rana ta tunawa da sojoji, ina bukatar dukkan yan Najeriya da su bayar da lokacinsu domin taya sojojinmu murna. Allah ya albarkaci rundunar sojin Najeriya, Rundunar sojin sama, rundunar sojin ruwa da dukkannin hukumomin tsaronmu.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel