Dala miliyan $44m ba su bace daga asusun hukumar NIA ba – Jami’in hukumar NIA

Dala miliyan $44m ba su bace daga asusun hukumar NIA ba – Jami’in hukumar NIA

- Hukumar NIA ta ce babu kudin da ya bace daga cikin asusun ajiyan ta

- Wani baban jami'in hukumar NIA ya ce kudaden da aka zargi sun bace suna nan ajiye a cikin shelkwatar hukumar

Babu kudaden da suka bace daga asusun hukumar lekan asiri (NIA) kamar yadda wasu kafofin labaru suka yada inji wani babban jami’in hukumar NIA.

A ranar Asabar wasu kafofin watsa labaru suka yada labarin cewa an sace makudan kudade da suka kai kimanin dala miliyan $44m daga asusun ajiyan hukumar NIA kwanaki biyu bayan an nada, Ahmed Rufa’i Abubakar a matsayin sabon daraekta janar na hukumar NIA.

Dala miliyan $44m ba su bace daga asusun hukumar NIA ba – Jami’in hukumar NIA

Dala miliyan $44m ba su bace daga asusun hukumar NIA ba – Jami’in hukumar NIA

Kama dala miliyan $43m da aka yi a cikin wani gida dake unguwar Ikoyi a jihar Legas mallakar matar tsohon daraekta janar na hukumar NIA, Ayo Oke, yayi sanadiyar sauke Oke daga kan mukamin sa.

KU KARANTA : Wammako ya tuhumi Ortom da Ishaku akan kashe-kashen da aka yi a jihohin su

Wani jami’in hukumar NIA ya fadawa manema labaru cewa da a cikin ofishin, Ayo Oke, aka ga kudaden da aka boye a cikin gidan Ikoyi, da babu matsala saboda ba a san hukumar lekan asiri da ajiye kudaden kasashen waje ba.

Ya ce dala miliyan $44m da kafofin watsa labaru suka ba da labarin cewa sun bace karya ne, har yanzu kudaden suna shelkwatar hukumar NIA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel