Hukumar NYSC ta dakatad horon yan bautan kasa da aka tura jihar Benuwe da Taraba

Hukumar NYSC ta dakatad horon yan bautan kasa da aka tura jihar Benuwe da Taraba

Hukumar bautar kasa, wato National Youth Service Corps ta ce ta dakatad shirin tura matasa sansanin bautan kasa da ta shirya gudanarwa ranan 16 ga Junairu zuwa 5 ga Fabrairu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin sada zumuntarta na Facebook ranan Lahadi, 14 ga watan Junairu, 2018.

Hukumar ta ce za ta sanar da sabon ranan kiran matasan da aka tura wadannan jihohin 2 domin horo.

Hukumar NYSC ta dakatad horon yan bautan kasa da aka tura jihar Benuwe da Taraba

Hukumar NYSC ta dakatad horon yan bautan kasa da aka tura jihar Benuwe da Taraba

Jawabin yace: “Hukumar NYSC tana sanar da dukkan masu shirin bautan kasa da aka tura jihar Benuwe da Taraba cewa an dakatad da zuwansu.

Za’a sanar da su sabon ranan da zasu je nan ba da dadewa ba.”

KU KARANTA: Fasto Tunde Bakare ya yi kakkausar suka a kan gwamnatin Buhari

Ga dukkan alamu, hukumar ta yi yanke wannan shawara ne bisa ga rikicin da ke faruwa a wannan jihohi guda biyu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel