Rikicin makiyaya: Gwamna Lalong ya mayar wa da tsohon gwamna Jonah Jang raddi

Rikicin makiyaya: Gwamna Lalong ya mayar wa da tsohon gwamna Jonah Jang raddi

- Cacar baki ta barke tsakanin tsohon gwamna Jang da gwamna mai ci Lalong

- Lalong ya ce kalaman Jang a kan makiyaya sun tabbatar da cewar ba zai daina munafurci ba

- Cacar baki ta balle tsakanin shugabannin ne a kan rikicin makiyaya da jihar ke fama da shi

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya mayar da amsa ga maganar da tsohon gwamnan jihar kuma Sanata a yanzu, Jonah Jang, a kan batun kirkirar wuraren kiwo domin makiyaya da niyyar kiyaye afkuwar rikici tsakaninsu da manoma a jihar.

An samu barkewar cacar baki ne tsakanin shugabannin biyu biyo bayan matakin da gwamnan Lalong ya dauka na kirkirar burtalin kiwo domin makiyaya. Sanata Jang ya soki wannan mataki da gwamnan ya dauka, yana mai bayyana cewar mutanen mazabar ba zasu yarda da kirkirar wa makiyaya burtali ba a garuruwansu tare da bukatar gwamnan ya nemi afuwar mutane jihar Benuwe bisa kalamin da ya yi na cewar tun farko ya shawarci gwamna Ortom da ya kirkiri burtali domin makiyaya saboda a samu zaman lafiya.

Rikicin makiyaya: Gwamna Lalong ya mayar wa da tsohon gwamna Jonah Jang raddi

Gwamna Lalong da tsohon gwamna Jonah Jang

Saidai a wata takarda da Darektan watsa labarai na gwamna Lalong, Samuel Emmanuel, ya saka wa hannu, gwamnan ya bayyana kalaman na Sanata Jang a matsayin nuna halinsa na munafurci da ba zai taba daina wa ba. Kazalika ya ce halin tsohon gwamnan na nuna halin wariya da kabilanci ya jawo kashe-kashe a jihar lokacin da yake gwamna.

DUBA WANNAN: Sabon rikici tsakanin Hausawa da wasu matasa ya kara barkewa a jihar Benuwe

"Lalong ya jajantawa mutanen jihar Benuwe a kan halin da suka tsinci kansu, kuma ya bayar da shawara ne kawai a kan hanyar da yake ganin za'a bi domin warware matsalar rikicin makiyaya da manoma. Akwai kyakykyawar fahimta tsakanin gwamna Lalong da Ortom na jihar Benuwe," kamar yadda yake a cikin takardar.

Jawabin ya kara da cewar, mutanen jihar Filato da na Najeriya ba zasu manta da kashe-kashen rayuka da aka samu ba a karkashin mulkin jam'iyyar PDP, tare da bayyana cewar Sanata Jang da jam'iyyar sa ta PDP na yin borin kunya ne kawai.

Ya kara da cewa gwamna Ortom da Lalong suna da akida irin ta shugaba Buhari, akidar warware rikici ta hanyar amfani da maslaha, domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel