Buhari ya gana da Saraki, Dogara a kan kashe-kashen Binuwai

Buhari ya gana da Saraki, Dogara a kan kashe-kashen Binuwai

- Shugaban Buhari ya gana da shugabannin majalisar tarayya a kan kashe-kashen jihar Binuwai

- A fadar shugaban kasa aka gudanar da taron a daren ranar Lahadi

- Shugaba Buhari ya kira wannan taro ne domin ya ba da cikakken bayani ga shugabannin na kokarin dawo da zaman lafiya a Binuwai

Shugaba kasa, Muhammadu Buhari , a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu da yamma ya gana da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da kuma Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , an gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa, Abuja, don tattauna kashe-kashen da aka yi a jihar Binuwai da sauran sassa na kasar.

Fadar shugaban kasa ta bayyana haka a cikin sakon da aka buga a kan shafinta na kafar sada zumunta ta Twitter, @NGRPresident.

Buhari ya gana da Saraki, Dogara a kan kashe-kashen Binuwai

Shugaba kasa, Muhammadu Buhari, tare da shugabannin majalisar tarayya

Sanarwar ta ce shugaba Buhari ya kira taron domin ya ba da cikakken bayani ga shugabannin majalisar tarayya na kokarin da ake yi na sake dawo da zaman lafiya a yankunan da ake rikici.

KU KARANTA: Kashe-Kashe: Buhari zai gana da shugabannin jihar Benue a yau

A yau Litinin kuma ake sa ran shugaban kasa zai tattauna da shugabannin jihar Binuwai a kan rikicin makiyaya a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel