Zamu yi amfani da karfi mu murkushe makiyaya - Gwamna Akeredolu

Zamu yi amfani da karfi mu murkushe makiyaya - Gwamna Akeredolu

- Gwamna Akeredolu ya gargadi Makiyaya da su guji tayar da hankalin jama'a a jihar Ondo

- Ya ce zasu yi amfani da karfi su murkushe makiyaya matukar suka yi yunkurin hakan

- Ya yi Alla-wadai da hare-haren da makiyayan ke kaiwa a wasu jihohin Najeriya

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya gargadi makiyaya da su guji tayar da hankalin jama'a a jihar sa.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin sa na kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Ya bayyana hakan ne yayin halartar taron addu'o'in tunawa da jami'an tsaro da suka mutu, wanda aka gudanar a Cocin St. David's Cathedral Anglican, dake Akure, babban birnin jihar Ondo.

Zamu yi amfani da karfi mu murkushe makiyaya - Gwamna Akeredolu

Gwamna Akeredolu
Source: Depositphotos

Akeredolu ya ce gwamnatin sa zata yi amfani da karfi a kan makiyayan matukar kokarin sulhu da su ya ci tura.

"Muna amfani da jami'an tsaro domin tattaunawa da makiyayan da kuma basu damar yin harkokin kasuwanci a jihar Ondo, amma idan suka suka sabawa yarjejeniyar da muka kulla, zamu yi amfani da karfi mu murkushe su," inji Akeredolu.

DUBA WANNAN: Sabon rikici tsakanin Hausawa da wasu matasa ya kara barkewa a jihar Benuwe

Kazalika gwamnan ya nuna bacin ransa bisa yawan kutse da makiyayan ke yi a gonar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Olu Falae, dake jihar, yana mai bayyana cewar gwamnatinsa ba zata yarda da duk wani nau'in aikin ta'addanci ba.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata saida gwamnan ya yi irin wannan gargadi a karamar hukumar Ifedore yayin halartar wani taro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel