Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba

Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba

- Femi Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta bi umurnin kotu ta saki El-Zakzaky da matarsa

- Ya ce gwamnatin tarayya ta saki ma’auratan

- Ya bayyana cewa sabanin ikirarin gwamnati, El-Zakzaky baida lafiya sannan kuma yana bukatar kulawar likita sosai

A ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu, Shahararren lauyan nan mai kare hakkin dan adam, Femi Falana (SAN), ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki shugaban kungiyar Shia, Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zainab.

Hukumar yan sandan farin kaya sun gurfanar da El-Zakzaky da matarsa a gaban yan manema labarai a makon day a gabata bayan ana ta yada jita-jitan mutuwarsu.

Punch ta ruwaito cewa Falana a wani jawabi da ya yi, ya bayyana ci gaba da tsare ma’auratan a matsayin abun da ya karya umurnin kotu sannan kuma bayyana su a kafofin watsa labarai a matsayin ba bisa doka ba.

Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba

Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba

Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta bi umurnin kotu ta saki ma’auratan daga hannun hukumar DSS.

KU KARANTA KUMA: Mazauna Jalingo sun shiga tashin hankali kan barazanar makiyaya na kai hari garin

Ya bayyana cewa sabanin ikirarin gwamnati, El-Zakzaky baida lafiya sannan kuma yana bukatar kulawar likita sosai.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da shawarar likitocin ido na cewa a fitar da El-Zakzaky kasar waje domin samun kulawa na musamman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel