Yaki da cin hanci da rashawa tamkar jihadi ne - Ibrahim Magu

Yaki da cin hanci da rashawa tamkar jihadi ne - Ibrahim Magu

Shugaban hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya watau Economic and Financial Crimes Commission a turance mai suna Mista Ibrahim Magu ya siffanta yaki da cin hanci da rashawa da jihadi wanda yace dole ne a yi shi.

Shugaban na hukumar da ke a matsayin mai rikon kwarya ya bayyana hakan ne a yayin bukin yaye dalibai a wata jami'a mai suna Fountain a garin Osogba, jihar Osun.

Yaki da cin hanci da rashawa tamkar jihadi ne - Ibrahim Magu

Yaki da cin hanci da rashawa tamkar jihadi ne - Ibrahim Magu

Jam'iar dai da kungiyar nan ta 'yan uwa musulmai ta NASFT ta yi bukin na yaye daliban ta ne a karo na bakwai sannan kuma ta yi shagulgulan cikar ta shekaru 10 da kafuwa.

Legit.ng ta samu kuma a wani labarin cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin karbar bakuncin shugabannin kabilun dake zaune a jihar Benue dake a arewa ta tsakiya yau a fadar sa dake garin Abuja babban birnin tarayya.

Mun samu dai cewa ganawar da shugaban zai yi da shugabannin jihar bai rasa nasaba da kashe-kashen kabilanci na fulani da makiyaya da akayi fama da shi a jihar a cikin satin da yagabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel