Wammako ya tuhumi Ortom da Ishaku akan kashe-kashen da aka yi a jihohin su

Wammako ya tuhumi Ortom da Ishaku akan kashe-kashen da aka yi a jihohin su

- Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya ce rashin adalci, tanadi da hangen nesa wajen zartar da dokar hana kiwo a fili ya janyo kashe kashe a jihar Taraba da Benuwe

- Sanata Aliyu Wammako yace adalci ne kadai zai warware matsalar rikicin makiyaya da manoma a kasar

Senata mai wakiltar mazabar Sokoto na tsakiya, Senata Aliyu Magatakarda Wamakko, yace kashe-kashen da aka yi jihar Benuwe da Taraba laifin gwamnonin jihohin ne, gwamna Samuel Ortom da Darius Ishaku.

Wammako yace rashin adalci, tanadi da hangen nesa wajen zartar da dokar hana kiwo a fili dan koran wasu yan asalin jihar da gwamnonin suka yi ya janyo kashe-kashe.

Wammako ya tuhumi Ortom da Ishaku akan kashe-kashen da aka yi a jihohin su

Wammako ya tuhumi Ortom da Ishaku akan kashe-kashen da aka yi a jihohin su

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wammako, ya ce, maimakon gwamnoni su nemi shawarar dattawa da masu fada aji wajen warware matsalar makiyaya da manoma a jihohin su, sai suka yanke hukuncin son zuciya da rashin adalci, gashi yanzu ala'amrin ya juya an fara kashe-kashe.

KU KARANTA : Kira ga Kristocin Najeriya : Kowa ya shiga siyasa gadan-gadan - Kungiyar CAN

Wammako yace rikicin makiyaya da manoma rikici ne ya dade ana yi, kuma rikicin ya kara muni a yanzu saboda yawan jama’a. Mafita anan shine yiwa kowa adalci tunda dokar kasa taba kowa yanci zama a ko’ina a fadin kasar.

Ya kuma yi Allah wadai da yunkurin da wasu yan siyasa da kafofin watsa labaru suke yi na takaita laifin kashe-kashen ga makiyaya kadai, ya ce an kashe makiyaya da dama a kauyuka da sace musu shanu amma babu wanda ke magana akan ta’adanci da ake musu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel