Na fara fyade ne sadda budurwa ta ta gudu ta barni - inji wani dan iska

Na fara fyade ne sadda budurwa ta ta gudu ta barni - inji wani dan iska

Wani matashi mai shekaru ashirin a duniya mai suna Abdullateef Ibrahim da jami'an 'yan sandan Najeriya suka kama shiyyar jihar Neja bisa laifin yiwa wata yarinya mai shekaru biyar a duniya fyade ya bayyana dalilin sa na yin hakan.

Matashin dai ya bayyana cewa ya fada cikin daudar yiwa 'yan yara fyade ne biyo bayan rabuwar da sukayi da budurwar sa a watannin baya.

Na fara fyade ne sadda budurwa ta ta gudu ta barni - inji wani dan iska

Na fara fyade ne sadda budurwa ta ta gudu ta barni - inji wani dan iska

Legit.ng dai ta samu daga bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ta Neja mai suna Muhammad Abubakar cewa tuni dai har bincike yayi nisa game da batun mutumen kuma da zaran ya kammala za su maka shi zuwa kotu domin hukunci.

A wani labarin kuma, Rahotannin da ke zuwa mana na nuni ne da cewa jami'an sojin saman Najeriya sun sanar da kammala siyo manyan jiragen yakin idasa fatattakar 'yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar dai ta bayyana cewa ta siyo jiragen yakin ne daga kasar Pakistan dake a yankin gabashin duniya bayan lokaci mai tsawo da ta dauka tana cinikin su.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel