Kashe-Kashe: Buhari zai gana da shugabannin jihar Benue a yau

Kashe-Kashe: Buhari zai gana da shugabannin jihar Benue a yau

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin karbar bakuncin shugabannin kabilun dake zaune a jihar Benue dake a arewa ta tsakiya yau a fadar sa dake garin Abuja babban birnin tarayya.

Mun samu dai cewa ganawar da shugaban zai yi da shugabannin jihar bai rasa nasaba da kashe-kashen kabilanci na fulani da makiyaya da akayi fama da shi a jihar a cikin satin da yagabata.

Kashe-Kashe: Buhari zai gana da shugabannin jihar Benue a yau

Kashe-Kashe: Buhari zai gana da shugabannin jihar Benue a yau

Legit.ng ta samu cewa wadanda ce cikin tawagar da za su tattauna da shugaban sun hada da shugabannin siyasa da na addinai da kuma sarakunan gargajiyar dake jihar.

Haka nan kuma mun samu cewa tawagar zata je ne a karkashin jagorancin gwamnan jihar Samuel Ortom.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin makon jiya ne dai kashe-kashen ramuwar gayayya suka ta'azzara a jihar a tsakanin makiyaya da kuma manoma lamarin da yayi matukar jan hankalin al'ummar Najeriya baki daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel