IBB ya yi gargadi a kan yawaitan kashe-kashe a Najeriya

IBB ya yi gargadi a kan yawaitan kashe-kashe a Najeriya

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Ibrahim Babangida, a ranan lahadi ya yi kira ga yan Najeriya da gwamnati da su kawo mafita daga halin rashin tsaro da kasar ke ciki.

Janar Babangida, wanda tsohon soja ne ya yi wannan jawabi ne a garinsa da ke Minna, jihar Neja.

Game da cewar jawabin, Babangida ya kwadaitar da yan Najeriya su nuna godiya bisa ga jaruntan jami'an tsaro ta hanyar taimakawa da kayayyakin jin dadi da kuma kula da iyalensu da suka bari.

Ya ce yanada matukar muhimmanci a wannan lokacin da kasar ke fuskantar kalubale irinsu ta'addanci, fadan kabila, garkuwa da mutane, dabbanci, da wasu harkokin rashin zaman lafiya.

IBB ya yi gargadi a kan yawaitan kashe-kashe a Najeriya

IBB ya yi gargadi a kan yawaitan kashe-kashe a Najeriya

“Mu hada kai mu baiwa tsaron kasa taimako ta hanyar fada musu abubuwan da ke faruwa domin taimakawa wadannan matsaloli."

“A matsayinmu na mutane, mu aiwatar da tarbiyyarmu wanda ya koya mana hakuri da juna, ayyukan kwarai da zaman lafiya."

KU KARANTA: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

"A karshe, mu daina maganganun sukan juna, zalunci da wasu abubuwan da ka iya tayar da hankalin jama'a da zub da jini."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel