Sai na mulki Najeriya ko ta wani hali – Inji wani babban Fasto

Sai na mulki Najeriya ko ta wani hali – Inji wani babban Fasto

Babban Faston cocin ‘Latter Rain Assembly’,Tunde Bakare yace ya samu wahayi daga ubangiji cewar zai zamo shugaban kasar Najeriya don kai ta tudun na tsira, ta kota wani hali.

Bakare ya bayyana haka ne yayin wani huduba na musamman daya shirya a cocinsa a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, inda yace ba lallai sai ta hanyar zabe ba, amma Allah ya zabe shi don ya ceci Najeriya.

KU KARANTA: Labari da Duminsa: Anyi jina-jina a sabon rikici tsakanin 'yan Gandujiyya da 'yan Kwankwasiyya a jihar Kano

Daily Trust ta ruwaito Fasto yana fadin: “Allah ya riga ya tsara sai nayi mulkin Najeriya, sai dai ban san yadda hakan zai tabbata ba, Allah ya bar ma kansa sani.”

Bakare

Fasto

Majiyar Legit.ng taruwaito shi ya cigaba da fadin “An sha samun yanayi yadda ake samun shuwagabanni ta hanyoyi daban daban, misali yadda George Washington ya zama shugaban kasar Amurka, da kuma Gerald Ford, haka zalika Richard Nixon, dukkaninsu sun shugabanci Amurka ba tare da tsayawa takara ba.”

Faston wanda a baya ya taba zama abokin takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2011, inda suka tsaya a mastsayin yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar CPC, yace Buhari ya gaza.

A cewar Faston, babban abinda ya tabbatar da gazawar gwamnatin Buhari shi ne rashin magance matsalar tsaron dake fusknantar kasar, na Fulani da makiyaya.

“Duk da matsalolin da ake fama dasu, muna jinjina ma gwamnati kan nasarar da take samu a kan Boko Haram, amma hare haren makiyaya dake aukuwa a garuruwan Benuwe, Taraba, Filato, Adamawa, Kaduna, Enugu, Edo, da Ogun, ya nuna Buhari ya gaza.” Inji Bakare.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel