Ana neman tsaida wani Dattiijo a matsayin Firayim Minista a Malaysia

Ana neman tsaida wani Dattiijo a matsayin Firayim Minista a Malaysia

A kasar Malaysia mun samu labari daga Jaridar AP cewa ana neman tsaida wani mai sama da shekaru 92 Mahathir Mohammad a matsayin ‘Dan takara a zabe mai zuwa na kasar.

Jam’iyyar adawa a Malaysia ta tsaida Mahathir Mohammad a matsayin ‘Dan takarar Firayim Minista a zaben kasar mai zuwa. Mahathir ya taba rike Firayim Ministan Kasar a baya. Har yanzu dai Mahathir din yana da farin jini a kasar.

Ana neman tsaida wani Dattiijo a matsayin Firayim Minista a Malaysia

Tsohon Shugaban Kasar Malaysia Mohathir

Najib Razak wanda shi ke mulkin Kasar yana fama da adawa a Malaysia daga 2013 bayan zargin da ke yawo a kan sa. Idan dai Mahathir ya samu mulkin Kasar, zai zama wanda ya fi kowa tsufa a shugabannin kasashen Duniya.

KU KARANTA: PDP za ta dawo mulki a 2019 saboda Atiku

Shugaban na Malaysia Razak ya tsige masu sukar sa har a cikin Gwamnatin sa; daga ciki har da wani Mataimakin Firayim Ministan kasar watau Mista Anwar Ibrahim da kuma Ministan Shari’a na kasar shekaru biyu da su ka wuce.

Mahathir yana cikin shugabannin da ya fi kowa dade a Duniya lokacin da yayi mulki a kasar. Mahathir ya mulki Malaysia na sama da shekaru 22 kafin ya sauka a 2003.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel