Karin matsayi : Kemi Adeosun ta samu mukami a UN

Karin matsayi : Kemi Adeosun ta samu mukami a UN

- Ministar tattalin Najeriya ta samu shiga a wani kwamitin UN

- An nada Kemi Adeosun a wani kwamitin fansho na Majalisar

- Kwamitin na UNJSPF na kula da fanshon wadanda su ka rasu

Ministar tattali ta Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari watau Kemi Adeosun ta samu shiga a Majalisar Dinkin Duniya watau UN kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Premium Times.

Karin matsayi : Kemi Adeosun ta samu mukami a UN

Ministar tattali ta samu shiga a Majalisar UN

Kemi Adeosun ta shiga cikin wani babban Kwamiti na Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da harkar fansho watau UNJSPF. Wani babban Jami’i na UN Jan Beagle ya tabbatar da wannan nadin mukami a makon nan.

KU KARANTA: Sarkin Kano Sanusi ya kare 'Yan Fulani

Ministar Najeriyar za ta yi shekara guda tana rike da wannan mukami kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana. An dauki wannan mataki ne bayan wani taro da aka gudanar kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Minista Adeosun ta amince da wannan mukami da aka ba ta. Kwamitin na kula da fanshon Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniyar da su ka rasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel