El-Zakzaky ya amince ya gana da manema labarai saboda DSS ta ce za a saki shi

El-Zakzaky ya amince ya gana da manema labarai saboda DSS ta ce za a saki shi

- Ibrahim El-Zakzaky ya yarda ya yi magana da ‘yan jaridu saboda alkawarin za a saki shi

- Falana ya ce El-Zakzaky ya yi jawabi da 'yan jaridu don karyata zargin cewa ya mutu

- Babban lauyan ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki shi ba tare da jinkiri ba

Femi Falana, babban lauya a Najeriya (SAN), ya ce Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar ‘yan Shi’a (IMN), ya yarda ya yi magana da manema labarai saboda an ce za’a saki shi.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Falana ya ce El-Zakzaky ya yi jawabi ne da 'yan jaridu karo na farko a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu don karyata zargin cewa ya mutu kuma yace yana samun sauki.

A cewar Falana, sashen hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS) ta shaida wa jagorancin kungiyar ‘yan Shi’a cewa gwamnatin tarayya ta shirya ta saki shi bayan shekaru biyu a tsare.

El-Zakzaky ya amince ya gana da manema labarai saboda DSS ta ce za a sake shi

Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar ‘yan Shi’a (IMN)

Lauyan ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki shi ba tare da jinkiri ba.

KU KARANTA: Na fara samun lafiya yanzu - Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky

Ya ce El-Zakzaky ya rasa idonsa na hagu kuma gwamnati ta ƙi amince da shawarar da kwararru suka bayar a kan a kai shi kasar waje don kare na dama.

Falana ya ce matar shugaban 'yan Shi'a tana cikin mawuyacin hali kuma wasu harsasai da ke cikin jikinta tun a ranar 14 ga watan Disamban shekarar 2015 a lokacin da sojoji suka kai hari a gidan su a Zaria ba a cire su ba har yanzu.

Ya ce, "Sabanin ikirarin cewa jagoran Shi'a yana cikin koshin lafiya, amma ga shi yanzu yana sanye da dauri a wuyansa wanda aka sa masa a lokacin da ya fadi a watan Disamba na bara”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel