Kwazon Buhari ya dusashe farinjinin jam'iyyar PDP na shekaru 16 - Oyegun

Kwazon Buhari ya dusashe farinjinin jam'iyyar PDP na shekaru 16 - Oyegun

- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif John Oyegun, ya yabi shugaba Buhari

- Ya ce kwazon shi a Ofis ya dusashe farinjinin jam'iyyar PDP a Najeriya

- Ya fadi haka ne yayin wani taro da ya halarta a jihar Abiya

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun, ya ragargaji shekaru 16 da jam'iyyar PDP ta yi tana mulkin Najeriya, yana mai bayyana su da shekaru na bakin mulki da danniya.

Oyegun ya bayyana cewar kwazon shugaba Buhari a Ofis na shekaru biyu ya fi duk wata rawar gani da jam'iyyar PDP zata iya bugun kirji da ita, yana mai cewar shekaru biyu kacal na mulkin Buhari sun dusashe duk wani farin jini da jam'iyyar PDP keda shi a Najeriya.

Oyegun ya yi wadannan kalamai ne a jihar Abiya inda ya halarci wani taron gangami jam'iyyar APC.

Kwazon Buhari ya dusashe farinjinin jam'iyyar PDP na shekaru 16 - Oyegun

Buhari da Oyegun

Shugaban jam'iyyar ya ce shugaba Buhari yana aiki tukuru domin cike gurbin gurbacewar mulki da jam'iyyar PDP ta yi a Najeriya.

A cewar Oyegun "Mun farfado da hanyoyin sufurin jirgin kasa, kuma muna daf da shawo kan matsalar wutar lantarki. Mun inganta Noma; muna iya noma shinkafar da zamu ci. Cikin shekarar nan kowa zai ga alfanun mulkin shugaba Buhari."

DUBA WANNAN: Bamu da masaniyar ko Buhari zai tsaya takara a 2019 - APC

"Zan sanar da shugaban kasa cewar mutanen jihar Abiya na bukatar ya kara tsayawa takara a zaben shekarar 2019," inji Oyegun.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Rochas Okorocha, ya nuna jin dadinsa da ganin dandazon magoya bayan jam'iyyar APC da suka halarci taron, yana mai bayyana cewar hakan alama ce dake nuna jam'iyyar APC ta samu karbuwa a yanki na 'yan kabilar Igbo, kudu maso-gabas.

Kazalika Okorocha ya ce shekarar 2019 tamkar dama ce ga 'yan kabilar Igbo su gyara kura-kurai da suka yi a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel