Da dumi-dumi: Hukumar soji ta sayi sabbin jiragen yaki 5 daga kasar Pakistan

Da dumi-dumi: Hukumar soji ta sayi sabbin jiragen yaki 5 daga kasar Pakistan

- Hukumar sojin saman Najeriya wato Nigerian Air Force (NAF) ta sami sabbin jiragen yaki 5

- Sabbin jirage na daga cikin jirage 10 da hukumar tayi oda daga kasar Pakistan a kwanakin baya

A yau Asabar, 14 ga watan Janairu, 2017 misalin karfe 7:45 na safe hukumar sojin saman Najeriya, ta samu karin jiragen yaki kirar 'Mushtak ilyushin 74' da tayi oda daga Kasar Pakistan. An kawo jiragen kai tsaye jihar Kaduna.

Da dumi-dumi: Hukumar soji ta sayi sabbin jiragen yaki 5 daga kasar Pakistan

Da dumi-dumi: Hukumar soji ta sayi sabbin jiragen yaki 5 daga kasar Pakistan

Shugaban sashen kayayyakin hukumar, Air Vice Marshal Bello Garba, ta tarbi wadannan jirage ne a madadin babban hafsan sojan hukumar, Air Marshal Sadique Abubakar.

Sojojin saman Najeriya da na kasar Pakistan ne suke halarce a wurin domin sauke jirage daga cikin jirgi.

KU KARANTA: Dubi wata karamar yarinya mai shudin idanu da ake zargi da maita

Bugu da kari, jami'an hukumar fasa kwabri ta Kwastam da hukumar shiga da fice suna halarce domin tabbatar da cewa anyi abin da ya kamata. Sabbin jiragen da za'a iya amfani da su wajen horon matukan jirgin yaki kuma jiragen yayi ne.

Sabbin jirage na daga cikin jirage 10 da gwamnatin tarayya tayi oda daga kasar Pakistan a shekarar 2016.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel