Yadda dala miliyan $44 suka kara bacewa daga cikin asusun hukumar NIA

Yadda dala miliyan $44 suka kara bacewa daga cikin asusun hukumar NIA

- Makudan kudade sun kara bacewa a cikin asusun hukumar NIA

- Nada Ahmed Rufai da shugaba Buari yayi a matsayin sabon shugaban hukumar NIA ya janyo cecekuce a Najeriya

Watanni biyu bayan an sauke, Ambassada Ayodele Oke, a matsayin Daraektan hukumar lekan asiri (NIA) kuma kwanaki biyu bayan an rantsar da Ahmed Rufa’i, a matsayin sabon daraektan janar na hukumar NIA ta kara fuskantar sabuwar bakadalar kudi inda dala miliyan $44m suka bace daga asusun hukumar.

Legit.ng ta samu labarin cewa an cire makudan kudaden ne a cikin asusun hukumar NIA kafin aka rantsar da sabon daraektan.

Yadda dala miliyan $44 suka bace a cikin asusun hukumar NIA

Yadda dala miliyan $44 suka bace a cikin asusun hukumar NIA

A makon da ya gabata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada da Ahmed Rufa’i, a matsayin sabon daraektan hukumar NIA.

KU KARANTA : PDP za ta dawo kan mulki idan aka tsayar da Atiku a matsayin takarar shugaban kasa a zaben 2019 - Kungiyar AGSG

Nadin Ahmed Rufa’i, a matsayin sabon shugaban hukumar NIA, ya janyo cecekuce a Najeriya, inda wasu suke zargin shugaban kasa da nuna bangaranci da bambamnci addini wajen ba da mukamai a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel