Rikcin Benuwe : Ortom ya ba Buhari, Osinbajo da sauran su laifin kai wa jihar sa hari

Rikcin Benuwe : Ortom ya ba Buhari, Osinbajo da sauran su laifin kai wa jihar sa hari

- Gwamnan jihar Benuwe ya ce sakacin Buhari, Osinbajo, NSA da Sfeto janar na yansanda ya sa a kai wa jihar Benuwe hari

- Samuel Ortom ya ce ya rubutawa Buhari Osinbajo NSA da Sfeto janar na yansanda wasikar gargadi akan yunkurin kawo wa jihar sa hari amma basu amsa

Gwamnan jihar Benuwe, Mista Samuel Ortom, ya fadawa kwamitin majalissar dattawa da suka ziyarci jihar dan binciken kisan gillan da akai yiwa mutane 53 a jihar cewa laifin Buhari, Osinbajo, NSA da Sfeto janar na yansanda na watsi da gargadin da ya musu akan yunkurin kai wa jihar sa hari.

Gwamnan ya ba jami’an tsaro laifin cigaba da kashe mutanen sa da makiyaya suke yi tun shekara 2008.

Ortom yace, kafin a kawo wa jihar Benuwe hari, ya taba rubutawa Osinbajo wasika a lokacin da yake mukamin mukaddashin shugaban kasa bayan Buhari ya tafi jinya kasa waje, cewa ana yunkurin kawo wa jihar sa hari.

Ortom ya fadawa majalissar dattawa cewa rikicin Benuwe laifin Buhari, Osinbajo, NSA da Sfeto janar na yansanda ne

Ortom ya fadawa majalissar dattawa cewa rikicin Benuwe laifin Buhari, Osinbajo, NSA da Sfeto janar na yansanda ne

Gwamnan yake duk kokarin da yayi na ganin cewa ya samu hankalin Osinbajo ta wasika bai yiwu ba.

KU KARANTA : Ya bindiga sunyi awon gaba da tsohuwar kwamishinan sufuri na jihar Bayelsa

Ortom yace, ya rubutawa Buhari wasika a lokacin da ya dawo jinya daga kasar Landan amma bai bashi amsa ba.

“Bayan haka na kara rubutawa mai ba da shawara a fannin tsaro, Monguno akan wannan al’amari shima bai amsa ba.

"A ranar 1 ga watan Oktoba na kara rubutawa Sfeto janar na yansanda wasika akan yunkurin kawo wa mutane na hari, shima bai amsa ba.

Ortom y ace har shugaban majalissar Dattawa da kakakin majaillsar wakillai ya rubuta musu wasika akan wannan al’amari amma babu wanda ya bashi amsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel