Sakamakon gwajin lafiyar shugaba Trump ya fito

Sakamakon gwajin lafiyar shugaba Trump ya fito

- An yi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, gwajin lafiya

- Wannan shine gwajin lafiyar sa na farko tun bayan hawansa mulki

- Cikakken rahoto zai fito ranar Talata

An yi wa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, gwaje-gwajen lafiyar sa a karo na farko tun bayan hawansa mulki. An gudanar da gwaje-gwajen ne ranar Juma'a da ta gabata.

An yanke shawarar yi WA Trump gwaje-gwajen ne bayan wani marubuci, Michael Wollf, ya wallafa wani littafi da yake nuna shakkun koshin lafiyar hankalin shugaba Trump.

Sakamakon gwajin lafiyar shugaba Trump ya fito

shugaba Trump

Saidai bayan kammala gwaje-gwajen, shugaban likitocin fadar white house, Ronny Jackson, ya tabbatar da cewar Trump din lafiyar sa kalau, babu wani abu dake damun shi.

DUBA WANNAN: Iran ta haramta koyar da turanci a makarantun firamaren kasar

Cikakken rahoton sakamakon gwaje-gwajen zai fito ranar Talata mai zuwa.

Masu zargin Trump da karancin lafiyar hankali na kafa hujja ne da irin yadda shugaban ke sakin baki tare da yin katobarar zancen da ko kananan yara masu wayo ba zasu yi ba.

Ko a cikin satin da ya kare saida Trump ya yi kalaman muzanci a kan kasashen nahiyar Afrika.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel