PDP za ta dawo kan mulki idan aka tsayar da Atiku a matsayin takarar shugaban kasa a zaben 2019 - Kungiyar AGSG

PDP za ta dawo kan mulki idan aka tsayar da Atiku a matsayin takarar shugaban kasa a zaben 2019 - Kungiyar AGSG

- Kungiyar Atiku Global Support Group (AGSG) ta bukaci PDP ta tsayar da Atiku a mastayin dan takaranta a zaben 2019

- AGSG ta ce Aiku ne kadai zai iya magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta

Kungiyar Atiku Global Support Group (AGSG) sun yi kira da jami’yyar PDP ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubukar, a matsayin dan takaranta a zaben 2019.

Kungiyar ta ce, Atiku ne kadai zai iya magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Atiku Abubakar zai tabbatar da zaman lafiya da hadin kan yan Najeriya, kuma zai samar da ayyuka da yawa idan ya zama shugaban kasa inji kungiyar.

PDP za ta dawo kan mulki idan aka tsayar da Atiku a matsayin takarar shugaban kasa a zaben 2019 - KungiyarAGSG

PDP za ta dawo kan mulki idan aka tsayar da Atiku a matsayin takarar shugaban kasa a zaben 2019 - KungiyarAGSG

Jagoran kungiyar AGSG, Gambo Jagindi, ya ce bai kamata Wazirin Adamawa ya sha wahalar samun tikitin takara a jam’iyyar PDP ba, saboda shine dan takara da ya cancanci samun kujerar.

KU KARANTA : Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Ya yaba da kokarin da gwamnan jihar Rivas da Ekiti, Ayodele Fayose suka yi wajen nuna wa Atiku goyon baya.

Gambo Jagindi, Atiku attajirin mai kudi ne da ba zai saci kudin yan Najeriya ko da ya zama shugaban kasa, babban burin sa shine tabbatar da yan Najeriya tabbatar da yan Najeriya sun samu zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel