LABARI DA DUMI-DUMI: Wike ya kori shugabannin kananan hukumomi 3 a Ribas

LABARI DA DUMI-DUMI: Wike ya kori shugabannin kananan hukumomi 3 a Ribas

- Gwamna Wike ya kori wasu shugabannin kananan hukumomi uku a jihar Ribas

- Ana zargin shugabannin da aikata laifin cin hanci da rashawa

- Shugabannin kananan hukumomin da lamarin ta shafa sun hada da karamar hukumaomin Fatakwal da Obio / Akpor da kuma Ikwerre

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya amince da dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi guda uku a jihar saboda zargin cewa suna tattara kudaden haram daga kamfanoni a yankunan su.

Shugabannin kananan hukumomi guda uku da lamarin ta shafa, kamar yadda wata sanarwa da hadimin gwamnan jihar, Saminu Nwakaudu, ya bayar a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu sun hada da karamar hukumaomin Fatakwal da Obio / Akpor da kuma Ikwerre.

"Dakatar da shugabanni zai fara ne nan da nan", in ji Mista Nwakaudu a cikin sanarwar.

LABARI DA DUMI-DUMI: Wike ya kori shugabannin kananan hukumomi uku a Ribas

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike

Har yanzu gwamnatin jihar ba ta gudanar da zaben kananan hukumomin ba. Gwamnan ne ya nada shugabannin wucen gadi na kananan hukumomin guda 23.

KU KARANTA: Zaben 2019 karshen yaki ga APC – Inji Rotimi Amaechi

Idan baku manta Legit.ng ta ruwaito cewa ministan sufuri, Rotimi Ameaci ya ce idan jam’iyyar APC a jihar ta kasa lashe kujerar gwamna na jihar a zabe ta shekarar 2019, za su koma gida su huta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel