Kungiyar dattawa Arewa ACF sun mayar wa Nwabueze martani akan sukar Buhari da yayi

Kungiyar dattawa Arewa ACF sun mayar wa Nwabueze martani akan sukar Buhari da yayi

- Ferfesa Ben Nwabueze ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kudirin mayar da Najeriya kasar musulmai

- Sekataren kungiyar Arewa ya ce bai da ce dattijo kamar Ferfesa Ben Nwabueze ya rika furta kalaman da zai raban kawanunan yan Najeriya ba

Kungiyar dattawan Arewa tayi kaca-kaca da, Ferfesa Ben Nwabueze, akan zargin da yayi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na yunkurin mayar da Najeriya kasar Musulunci.

Ben Nwabueze, yace shugaba Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa ne dan mayar da Najeriya kasar musulmai.

Ben, yace Buhari ya nada musulmai yan Arewa a matsayin shugabanin hukumomin jami’an tsaron Najeriya da wasu muhimman hukumomi, wanda ya kunshi, runduanr soji, yansanda, Kwastom da sauran su, yana cikin kudirin mayar da Najeriya kasar Musulmai.

Kungiyar dattawa Arewa ACF sun mayar wa Nwabueze martani akan sukar Buhari da yayi

Kungiyar dattawa Arewa ACF sun mayar wa Nwabueze martani akan sukar Buhari da yayi

Sekatare janar na kungiyar ACF, Anthony Sani, ya mayar Nwabueze martani da cewa, duk da raunin gwamnatin Buhari a wasu fannoni, manufar sa na tabbatar da adalci da zaman lafiya dan cigaban kasar mai kyau ne.

KU KARANTA : Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Sani y ace mutum mai matsayi irin na, Nwabueze, bai kamata yana furta kalaman da zai ya raba kawunan al’ummar kasa ba.

Sakataren ACF ya ce adawa a kowace dimokradiyya yana da kyau amma ba adawan nuna son zuciya ba.

Sani yace bai taba tunani dattijo kamar, Ferfesa Nwabueze, zai iya furta irin kalaman da yayi ba, ganin cewa shugaban rundunar sojin Najeriya da hafson sojojin ruwa ba musulmai bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel