Kalaman batanci da ake zargin Buhari ya rubuta a shafin sa na tuwita akan makiyaya karyace – Fadar Shugaban kasa

Kalaman batanci da ake zargin Buhari ya rubuta a shafin sa na tuwita akan makiyaya karyace – Fadar Shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta ankarar da yan Najeriya akan shafin tuwita na bogi dake amfani sunan Buhari

- Shafin tuwita na bogi dake amfani da sunan Buhari yana wallafa kalaman batanci dan bata shugaban kasa a idanun mutane kasar

Fadar shugaban kasa ta janyo hankalin yan Najeriya akan wata shafin tuwita na bogi dake amfani da sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa a fannin watsa labaru, Femi Adesina yace shafin yana ta wallafa jawabai da ya nuna shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yana goyon bayan hare-haren ta’adanci da Fulani makiyaya su ke yi da sunan kare kan su.

Kalaman batanci da ake zargin Buhari ya rubuta a shafin sa na tuwita akan makiyaya karyace – Fadar Shugaban kasa

Femi Adesine yace wannan aikin makiyan Najeriya ne da basa son zaman lafiya da cigaban kasar.

KU KARANTA : Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da hare-haren ta’adanci da makiyaya suke yi inji Adesina.

Shugaban kasa, ya tsaya a manganar sa na farko, da ya ba da umarnin kama masu kashe-kashe a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel