Jama'a sun hurowa Shugaban kasa Buhari wuta kan batun tazarce

Jama'a sun hurowa Shugaban kasa Buhari wuta kan batun tazarce

Yanzu haka mutane da dama sun fara tofa albarkacin su game da neman ake fitowa takarar Shugaban kasa da ake nema Shugaba Muhammadu Buhari yayi a zabe mai zuwa.

Gwamnonin APC na Arewa cikin su akwai Nasir El-Rufai, Abdullahi Ganduje, Yahaya Bello, Ibrahim Geidam, MA Abubakar da wasu takwarorin su sun nemi Shugaba Buhari ya sake takara wanda hakan ya raba kan Jama’ar kasar a halin yanzu.

Jama'a sun hurowa Shugaban kasa Buhari wuta kan batun tazarce

Gwamnonin Arewa sun nemi Shugaban kasa Buhari ya zarce

Gwamnonin Arewa sun gana da Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Juma'ar nan A Abuja inda su ka nemi Shugaban ya sake fitowa takara a 2019. Da dama daga cikin 'Yan adawa da wasu 'Yan APC sun soki wannan mataki na Gwamnonin.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya bayyana abin da zai faru idan aka fadi zaben 2019

Wani Sanatan Jihar Kaduna Shehu Sani yace a lokacin da ake fama da kashe-kashe da rikici iri-iri a Kasar kurum sai aka ji ana neman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi tazarce ya nuna cewa Shugabannin sun rasa imanin su da tausayin Jama'a.

Gwamna Ayo Fayose wanda yake adawa da Gwamnatin ya lissafo matsololin da ake fama da su amma Shugaban kasar na nema ya zarce a 2019. Har yanzu dai Fadar Shubaban kasa ba tace komai ba amma Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yace su na kan bakan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel