Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

- Jam’ian tsaron Najeriya sun gano wata sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

- Bincike ya nuna a cikin sansanin ake horar da yan fashi da makamai da masu garkuwa da mutane

Jam’ian tsaron Najeriya sun gano wata sansanin horar da sojoji na bogi a cikin garin Opokgu dake jihar Benuwe a yankin Arewa na tsakiya.

Bincike ya nuna a sansanin ake horar da yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane don a basu kudin fansa da sauran laifuka.

Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Jami'an sojoji na bogi

Jam’ian tsaron Najeriya sun bankado sansanin horar da sojoji na bogi a jihar Benuwe

Jam’ian sojoji na bogi

Binciken da jami’an tsaro suka gudnar ya nuna babu Fulani makiyaya ko daya a cikin mutunen da aka kama a cikin sansanin sojojin bogi da jami’an tsaro suka gano.

KU KARANTA : Taron zaman lafiya da mababanta addinai : Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci Buhari yayi koyi da Ganduje

A ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, 2018, aka birne mutane 56 da ake zargin Fulani makiyaya sun musu kisan gilla a jihar Benuwe.

Wannan al’amari ya sa rikici ya barke a ranar Asabar a birnin Makurdi yayin da masu gudanar da zanga-zanga suka fara kone-kone amma jami'an tsaro sun samu nasarar kwantar da tarzomar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel