Gwamnatin Legas ta haramta ayyukan masu amalanke a jihar

Gwamnatin Legas ta haramta ayyukan masu amalanke a jihar

- Gwamnatin jihar Legas ta haramta ayyukan masu amalanke da baro

- Sakataren gwamnatin jihar ya ce ci gaba da ayyukan masu amalanke za ta zama wani abin barazana ga nasarar wani sabon shirin gwamnati

- An umarce hukumomin tsaro a jihar su kama wadanda aka gano su kaita dokar

Gwamnatin jihar Legas a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu ta sanar cewa ta dakatar da ayyukan duk masu amfani da amalanke da baro, ta bayyana cewa ayyukan su yana haddasa kalubale ga yanayin muhalli a fadin jihar.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, sakataren gwamnatin jihar, Tunji Bello, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a Legas.

Mista Bello ya bayyana cewa, a karkashin wani sabon shirin tsabtace muhalli wato ‘Cleaner Lagos Initiative’ na gwamnatin jihar, ci gaba da ayyukan masu amalanke za ta zama wani abin barazana ga nasarar wannan shirin.

Gwamnatin Legas ta haramta ayyukan masu amalanke a jihar

Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode

Ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa masu turan amalanke suna da alhakin mafi yawa dangane da zubar da shara ba bisa ka'ida ba a cikin magudanar ruwa da kuma kan tituna a cikin dare wanda ya haddasa ambaliyar ruwa.

KU KARANTA: Zaben 2019 karshen yaki ga APC – In ji Rotimi Amaechi

Mista Bello ya ce bayan haka, mutanen sun zama barazana ga harkokin tsaro a jihar.

"Abin da gwamnatin jihar ta gano shine cewa wadannan mutane suna amfani da dare don aikata ayyukan da ba daidai ba".

"An umarce hukumomin tsaro a jihar don tabbatar da cewa an kama wadanda aka gano har yanzu suna aikin a kuma hukunta su bisa ga dokar muhalli na jihar".

"Dokar ta kuma shafi mazauna wadanda ke amfani da su”, in ji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel