Zaben 2019 karshen yaki ga APC – Inji Rotimi Amaechi

Zaben 2019 karshen yaki ga APC – Inji Rotimi Amaechi

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce jam’iyyar APC ba za ta dora wani dan takara a kan ‘ya’yanta ba kuma ya bayyana babban zaben shekarar 2019 a matsayin karo na karshe ga APC.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana babban zabe ta shekarar 2019 a matsayin karo na karshe ga ‘ya’yan jam’iyya mai mulki ta APC.

Amaechi ya bayyana wannan ne a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, a lokacin bikin liyafa wanda aka shirya masa a matsayin uban kungiyar matasa na Ikwerre wato Ikwerre Youth Movement (IYM) a babban sakataren kungiyar na Isiokpo da ke yankin karamar hukumar Ikwerre na jihar Ribas.

Legit.ng ta tattaro cewa, ministan wanda kuma shine shugaban jam’iyyar APC a yankin kudu maso kudu ya ba da tabbacin cewa jam'iyyar APC za ta baiwa kowane dan jam’iyyar ‘yancin su, cewa ba za ta dora 'yan takara a zaben fidda gwani ba.

Zaben 2019 karshen yaki ga APC – Inji Rotimi Amaechi

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi

Ya ce: "Zaben shekara ta 2019, musamman na gwamna, shine na karshe, idan muka ci nasara, za mu kwace mulkin jihar Ribas. Idan kuma muka rasa, za mu koma gida mu huta”.

KU KARANTA: Ka manta da 2019, magance rikicin makiyaya shine muhimmi a gabanka - Shehu Sani ga Buhari

"Ba za mu dora wani dan takara ba. Duk wanda ke da sha’awar neman wani matsayi, kamar shugabancin kananan hukumomi, ya shiga zaben fidda gwani, kuma duk wanda ya ci nasara zai zama dan takara na jam’iyyar”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel