Jihar Bauchi ta na kashe fiye da N900m wurin samar da ruwa a shekara

Jihar Bauchi ta na kashe fiye da N900m wurin samar da ruwa a shekara

- Daraktan Ma'aikatar Ruwa na Jihar, Injiniya Aminu Aliyu Gital ne ya bayyana hakan

- Ya ce gwamnatin Jihar ta riga ta tanadi duk abun da a ke bukata na samar da ruwa

- Sai dai kuma al'umma ba ta iya biyan kudin ruwa wanda bai taka kara ya karya ba

Jihar Bauchi ta na kashe kusan naira biliyan 1 a shekara wurin samar da ruwa ga al'ummar ta. Injiniya Aminu Aliyu Gital, Daraktan Ma'aikatar Ruwa da Magudanan Ruwa, shi ne ya bayyana haka yayin wani taron Ma'aikatar da Kungiyoyin 'yan Kasuwa.

Jihar Bauchi na kashe sama da N900m don samar da ruwa duk shekara

Jihar Bauchi na kashe sama da N900m don samar da ruwa duk shekara

Gital ya bayyana cewan an yi taron ne don wayar da kan al'umma game da muhimmancin biyan kudin ruwa. Ya ce ta hanyar biyan kudin ruwan ne gwamnati za ta samu damar cigaba da samar da shi.

DUBA WANNAN: Gobara ta kara barkewa a kasuwar katako na Ibadan, ta cinye shaguna 100

Ya ce gwamnati ta riga ta samar da komai na tsabtace ruwan da tafiyar da shi ga al'umma. Dan abun da a ke bukatan al'umma ta biya da shi ne a ke sayen sindaran tsabtan da sauran dan kananan hidimomi.

Sai dai kuma, abun takaici a kudin ruwa da bai wuce naira miliyan 30 da al'umma za ta biya ba, da kyar jama'a ke iya biyan naira miliyan 20.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel