Ka nemi afuwar zagin da kayi mana - Kungiyar Taryyar Afrika ta fadawa Trump

Ka nemi afuwar zagin da kayi mana - Kungiyar Taryyar Afrika ta fadawa Trump

- Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci shugaban Amurka Donald Trump ya janye kalamar da ya fadi

- Kungiyar ta ce tayi mamaki da takaicin jin irin wannan kalaman daga bakin shugaban

- Kungiyar tace gwamnatin Shugaba Trump tayi ma Afrika mummunan fahimta kuma ya zama dole a tattauna kan batun

Kungiyar Tarayar Afrika ta yi Allah-wadai da kalaman batanci da aka ruwaito Shugaban Amurka Donald Trump ya furta game da kasashen Africa da ma wasu kasashen daban kuma ta bukaci shi ya janye maganan.

Tawagar Kungiyar Tarayyar Afrikan da ke birnin Washington DC ta bayyana takaici da bacin ranta a kan kalaman, ta kuma kara da cewa gwamnatin shugaba Donald Trump tayi wa 'yan Afirka mummunan fahimta.

Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka ta bukace Trump ya janye kalaman battancin da ya fada kan Nahiyar

Kungiyar Tarayyar kasashen Afirka ta bukace Trump ya janye kalaman battancin da ya fada kan Nahiyar

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi ram da matsafa 'yan yankan kai a Osun

An ruwaito cewa shugaban na Amurka ya furta kalaman ne a ranar Alhamis yayin da ake gudanar da taro kan dokokin kiyaye iyakan kasar sai dai shugaban ya ce bai abin da ya fada ba kenan.

A yayin da wasu Sanatoci biyu yan jam'iyyar sa ta Republican suka mara masa baya cewa bai fada hakan ba, Sanata Dickk Durbin na jam'iyyar Democrat ya tabbatar da cewa Trump ya fadi kalmar.

Kungiyar Tarayyar Afrikan tace kalaman nasa ya ruguje mutunci da kima da nahiyar ta Afirka ke danganta kasar na Amurka dashi a baya kuma ta ce akwai bukatan a zauna domin tattaunawa kan batun da wannan sabuwar gwamnatin na Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel