2019: Buratai ya gargadi jami'an sojoji su nisanci harkokin siyasa

2019: Buratai ya gargadi jami'an sojoji su nisanci harkokin siyasa

- Tukur Buratai ya gargadi jami'an sojojin Najeriya su nisanci harkokin siyasa

- CAOS ya bukaci jami’an su bar harakar siyasa ga 'yan siyasa, su mayar da hankali ga aikin da suka zaba

- Buratai ya gargadi masu amfani da jami’an sojoji don dalilai na siyasa su kaurace wa wannan hali

Babban hafsan sojojin kasar (COAS), Leftanal Janar Tukur Buratai, ya bayar da gargadi ga dukkan jami'ai rundunar soji na Najeriya cewa su nisanci harakar siyasa.

Buratai, wanda kwamanda na ‘Infantry Corps’, Manjo Janar Lamidi Adeosun ya wakilta, ya ba da sanarwar a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, bayan bikin kammala karatun jami'ai wadanda suka yi karatu a kan horarwa da dabarun jagoranci na 64 RC da SSC 44 a 20 Sertiyan Battalion Serti, wanda ke Taraba.

Babban hafsan ya ce, "Ku nisanci harakar siyasa, ku bari ga 'yan siyasa kuma ku mayar da hankali ga aikin da kuka zaba".

2019: Buratai ya gargadi jami'an sojoji su nisanci harkokin siyasa

Babban hafsan sojojin kasar (COAS), Leftanal Janar Tukur Buratai

Legit.ng ta tattaro cewa CAOS ya umarci jami'ai wadanda suka kammala karatu na yin amfani da ilimin da kuma kwarewa da suka samu a yayin horon don taimaka wajen magance matsalolin tsaro na yanzu a kasar.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi ram da matsafa 'yan yankan kai a Osun

Buratai ya ce: "Yana da muhimmanci a bayyana cewa, nasarar da rundunar sojojin Najeriya ta samu na kwanan nan a arewa maso gabas da sauran ayyukan tsaro na gida a duk fadin kasar ana sa ran zai kalubalantar masu aikata laifin”.

Yayin da ya bukaci su yi jagoranci ta misali, ya lura cewa "Irin wadannan kalubalen sun kasance ne game da sace-sacen mutane, kashe-kashe, fashi da makami da sauran ayyukan ta'addanci".

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar soji, Sani Usman ya ce: "Wannan shi ne wata sanarwa ga al’ummar kasar cewa babban hafsan sojojin kasar, ya samu bayani cewa wasu ‘yan siyasa suna kokarin amfani da wasu jami'anta don dalilai na siyasa da ba a bayyana ba”.

"Bisa wannan rahoto ya sa CAOS ya gargadi irin wadannan mutane su kaurace wa wadannan ayyukan”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel