Gobara ta kara barkewa a kasuwar katako na Ibadan, ta cinye shaguna 100

Gobara ta kara barkewa a kasuwar katako na Ibadan, ta cinye shaguna 100

- Gobarar ta ci shaguna 100 a inda ta halaka dukiya masu dimbin yawa

- Ba don daukin gaggawa daga 'Yan Kwana-Kwana ba, da kasuwar ta kone gaba daya

- Wannan gobara ta faru shekaru 2 kenan bayn faruwar wacce ta ci fiye da shaguna 300

Gobara ya kara barkewa a wani sashi na kasuwar katako na Ibadan da ke Alaro na yankin Sango, wanda a ka fi sani da Kasuwar Katako ta Igbajo. Gobarar da ta barke ne da misalin karfe 2 na dare na jiya, ya ci shaguna 100 a inda a ka yi asarar kayakin miliyoyin naira.

Gobara ta kara barkewa a kasuwar katako na Ibadan, ta cinye shaguna 100

Gobara ta kara barkewa a kasuwar katako na Ibadan, ta cinye shaguna 100

Ba don daukin gaggawa daga Hukumar Kwana-Kwana ba, da gobarar ta ci kasuwar gaba daya har ma ta hada da gidajen da ke makotaka da ita. Wannan gobara ta faru shekaru 2 kenan bayan faruwar gobarar da ta ci fiye da shaguna 300.

DUBA WANNAN: Yadda wata 'yar shekaru 14 ta taimakawa 'yar Chibok wajen kubuta daga Boko Haram

Wadanda su ka fara halartar wurin gobarar sun hada da Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar, Mista Abiodun Odude da DPO na Sango da kuma Mukaddashin Ciyaman din Karamar Hukumar da yankin ta ke.

Mai magana da yawun Hukumar 'Yan Sanda, Adekunle Ajisebutu, ya shaidawa Jaridar Saturday Sun cewar Kwamishinan ya ziyarci wurin ne don duba irin barnar da wutar ta yi. Kwamishinan ya kuma tabbatar wa 'yan kasuwar da cikakken tsaro da binciken musabbabin wutar.

Da wakilin Jaridar Saturday Sun ya ziyarci wurin, ya tarar da wadanda gobarar ta shafa su na jimami da takaicin hakan. Su na kuma tsintar dan abun da gobarar ta rage.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel