Rushe Rumfuna: Gwamna Obiano ya fusata masu sana'ar karuwanci a jihar Anambra

Rushe Rumfuna: Gwamna Obiano ya fusata masu sana'ar karuwanci a jihar Anambra

Rushe gine-gine da rumfuna da basa bisa ka'ida akan babbar hanyar Onitsha zuwa Enugu da gwamnatin jihar Anambra ke gudanarwa ya kawar da wasu masu sana'ar karuwanci.

A yayin ganawa da manema labarai na jaridar Southern City a ranar Juma'ar da ta gabata, shugaba ta masu sana'ar karuwanci a yankin, Linda, ta soki gwamnan jihar, Cif Willie Obiano a sakamakon umarnin da bayar na yin rusau a yankin da suka hadar har da rumfunansu.

Take cewa, "shin yanzu wannan wuri kwatsam ya zamto gine-ginen da ba bisa ka'ida ba? Wannan shine wurin da muka kadawa Obiano kuri'un mu a zaben ranar 18 ga watan Nuwamba a shekarar da ta gabata."

"Ina dalilin da ya sanya ba a rushe rumfunan kafin zabe ba? Gwamna bai yi la'akarin ba mu sanarwa kafin zartar da wannan hukunci, kuma hakan bai dace domin kuwa ba a kare mana hakkokinmu a matsayin mu na bil Adama ba."

Gwamna Willie Obiano

Gwamna Willie Obiano

"Saboda haka muna nan babu wanda ya isa ya kore mu daga wannan wuri, kuma zamu sake gina rumfunan mu domin ci gaba da sana'o'in mu."

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Obiano ya bayar da umarni ga hukumar raya karkara da ci gaban al'umma, jami'an 'yan sanda, sojin kasa da kuma hukumomin tsafta akan su kawar da duk wani gini da baya bisa ka'ida a fadin jihar.

KARANTA KUMA: Takardun Boge: Kwalejin ilimi ta dakatar da ma'aikatan ta 500 a jihar Abia

Babban mai baiwa gwamnan shawara akan harkokin tsaro na jihar, Cif Chikodi Anara, ya tabbatar da rusau a jihar, inda yace mazauna sun gurbata yankunan da bayan gari da tarin shara.

Gwamnatin jihar ta shawarci mazauna wannan rumfuna a Awka, Onitsha, da kuma Nnewi akan su tattara ina-su-ina-su domin gwamnatin ba za ta amince da wasu gine-gine ba a yankunan.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel