Taron zaman lafiya da mababanta addinai : Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci Buhari yayi koyi da Ganduje

Taron zaman lafiya da mababanta addinai : Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci Buhari yayi koyi da Ganduje

- Gwamnatin jihar Kano ta gudanar da taron zaman lafiya da mababanta addinai (Inter-faith) karo na biyu a Kano

- Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi koyi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Gabduje ya gudanar da taron zaman lafiya da mababanta addinai a kasar

Gwamnatin jihar Kano ta gudanar da taron zaman lafiya da mababanta addinai (Inter-Faith) karo na biyu a ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, 2017 a birnin Kano.

Sanannen malamin addinin musulunci kuma shugaban hukumar Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya yaba wa gwamnan jihar Kano akan gudanar da wannan muhimmin taro.

Taron zaman lafiya da mababanta addinai : Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci Buhari yayi koyi da Ganduje

Taron zaman lafiya da mababanta addinai : Sheikh Aminu Daurawa ya shawarci Buhari yayi koyi da Ganduje

Sheikh Aminu Daurawa yayi jawabi akan muhimmanci zaman lafiya tsakanin musulmai da wanda ba musulmai da kuma illar daukan doka a hannu.

KU KARANTA : 'Yar jarida ta raunata wani dan sanda yayin zanga-zangan ma'aikata a Kaduna

A karshe, shehin mallamin ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi koyi da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Gabduje ya gudanar da irin wannan taro na kasa baki daya.

A cikin wadanda suka halarci taron akwai gwaman jihar Kano, Abdullahi Ganduji, gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, wakilin sarkin Kano, mai martaba Sarki Sanusi na II, wato mai martaba Ciroman Kano, shugabaninin addinin musulunci da na Krista, da shugabannin Kabilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel