Zabe: Kotu ta soke hukuncin da ya bayyana Okonkwo na PDP a matsayin sanata

Zabe: Kotu ta soke hukuncin da ya bayyana Okonkwo na PDP a matsayin sanata

- Kotu ta soke hukuncin da ya bayyana Okonkwo na PDP a matsayin sanata na jihar Anambra

- Alkalin kotun ya bayyana cewa Okonkwo ya batar da shi don ya yanke hukuncin

- Kotun a baya ta umurci INEC ta gabatar da takardun shaida ga Okonkwo a matsayin wanda ya yi nasara a zaben

Babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu ta soke shari'ar da ta yanke wa Dokta Obiora Okonkwo na babban jam'iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar sanata na jihar Anambra ta tsakiya a majalisar dattijai.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , mai shari'a John Tsoho ya bayyana cewa Okonkwo ya batar da shi don ya yanke hukuncin.

Wannan hukuncin ta ba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) damar gudanar da wani zabe a yau Asabar, 13 ga watan Janairu.

Zabe: Kotu ta soke hukuncin da ya bayyana Okonkwo na PDP a matsayin sanata

Babbar kotun tarayya

KU KARANTA: Jam’iyyar ADP ta ki amince da tsarin zaben 2019 da INEC ta fitar

Alkalin kotun a hukuncin da ya bayar a ranar 13 ga Disamba, 2017, ta umurci INEC ta gabatar da takardun shaida ga Okonkwo a matsayin wanda ya lashe zabe kuma ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Dakta Bukola Saraki, ya rantsar da shi nan da nan don ya cika gurubin wanda aka dakatar tun shekarar 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel