'Yan bindiga sun tarwatsa kan wani mutum a birnin Ibadan

'Yan bindiga sun tarwatsa kan wani mutum a birnin Ibadan

Wasu 'yan bindiga dadi sun kashe wani mutum Baba Jide, a ranar Juma'ar da ta gabata dake zaune a cikin motarsa daura da mashigar kwalejin ilimi ta birnin Ibadan a jihar Oyo.

Wani mashaidin wannan ibtila'in da abin ya faru a gabansa ya bayyana cewa, 'yan ta'addan sun tarwatsa kan mutumin ne ta yadda ko halittarsa ba a iya ganewa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an tsinci gawar Jide ne a cikin motarsa kirar Volkswagen mai lamba FC 996 APP, da sanyin safiyar ranar Asabar ta yau.

'Yan bindiga sun tarwatsa kan wani mutum a birnin Ibadan

'Yan bindiga sun tarwatsa kan wani mutum a birnin Ibadan

Legit.ng ta fahimci cewa, matsayar da motar take akan hanya tare da launin jini a gilashin motarsa ne ya dauki hankalin mutane a safiyar ta yau.

KARANTA KUMA: Hotunan wasu iyaye da suka nuna goyon bayansu ga gwamna El-Rufa'i

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai, inda yace tuni an garzaya da gawar mamacin zuwa asibitin Adeoyo na jihar domin ci gaba da bincike da ya riga da kan kama.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abiodun Odude, ya umarci reshen leken asiri na hukumar akan bin diddigi wajen gano ainihin masu hannun aikata wannan ta'addanci.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel