Ya saci babur don ya sayar ya biya sadaki, yayi tsautsayin angwanci a hanya

Ya saci babur don ya sayar ya biya sadaki, yayi tsautsayin angwanci a hanya

- Wani barawo da ya sace mashin don gudanar da hidimar auren sa ya gamu da sakayya tun kafin ya yi nisa

- Mota ta kwashe shi yayin da ya nemi fecewa da mashin din, ya fado ya karya kafar sa

- Da kyar ya tsira da ran sa don kuwa ma su fushi da fushin wasu sun yi zimmar babbake shi da ran sa

A ranar Talata ne mota ta kwashe wani barawon babur mai suna Yunus Suleiman a kan titin Murtala Muhammad a Illorin na Jihar Kwara. Suleiman ya gamu da wannan sakayya ne yayin da ya ke kokarin fecewa da babur din, a inda ya fado ya karya kafar sa.

Ya saci babur don ya sayar ya biya sadaki, yayi tsautsayin angwanci a hanya

Ya saci babur don ya sayar ya biya sadaki, yayi tsautsayin angwanci a hanya

Yayin da 'yan kallo da masu fushi da fushin wasu su ka yo kan Suleiman da zimmar babbake shi da ransa, sai ya amsa laifin ya kuma yi nadamar abun da ya aikata. Ya kuma roke su da su taimaka su bar sa da ran sa.

KU KARANTA: Bana goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato - Jonah Jang

Da kyar dai ya tsira da ran sa, a ka mika shi hannun 'yan sanda. Suleiman ya bayyana cewan dole ce ta sa shi satar mashin din. A cewar sa, ya sace mashin din ne don samun kudin hidimar auren sa da ya matso.

Dan Sanda mai magana da yawun Hukumar, Ajayi Okasanmi, ya bayyna cewan Suleiman dan asalin garin Kishi ne na Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar. Ya kuma ce an bude bincike game da lamarin ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel