Sanya Ekwueme a makwanci: Gwamnonin Kudu maso Gabas sun gana a jihar Enugu

Sanya Ekwueme a makwanci: Gwamnonin Kudu maso Gabas sun gana a jihar Enugu

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, gwamnonin Kudu maso Gabashin kasar nan suka gana da juna dangane da yanke shawarwari akan shirye-shiryen da za a gudanar wajen bikin sanya tsohon shugaban kasa, Dakta Alex Ekwume a makwancinsa.

Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar 19 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, inda za a rufe shi a ranar 2 ga watan Fabrairun 2018 kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

A yayin ganawa da manema labari bayan ganawar tasu, shugaban gwamnoni Kudu maso gabas kuma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bayyana cewa, samun nasara wajen sanya mahaifinsu marigayi Ekwueme a makwanci ya rataya ne a wuyansu.

Baya ga gwamna Umahi, gwamnan jihar Enugu; Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Abia; Okezie Ikpeazu da kuma gwamnan jihar Anambra; Willie Obiano sun halarci taron.

Alex Ekwueme

Alex Ekwueme
Source: Depositphotos

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, bai halarci taron ba inda mataimakinsa Eze Madumere ya wakilce shi.

KARANTA KUMA: Shugaban shi'a El-Zakzaky bai mutu ba, yana nan a raye - IMN

Umahi ya bayyana cewa, Okorocha bai samu damar halartar taron ba sakamakon wata ziyarar aiki da ta sanya ya fice gaba daya daga yankin Kudu maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa, gwamnonin sun yi nazari dangane da kasafin kudin da za batar wajen sanya dattijon na Najeriya a makwancinsa.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel