Rikicin Makiyaya: Lalong karya yake, na kalubalance shi a wayan tarho - Samuel Ortom

Rikicin Makiyaya: Lalong karya yake, na kalubalance shi a wayan tarho - Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya ce takwararsa na jihar Flato, Simon Lalong bai gargadeshi akan dokar hana kiwo ba

A ranan Alhamis, Lalong ya ce ya gargadi Ortom a kan kafa dokan hana kiwo a fili a jihar.

Amma ranan Juma'a yayinda ya karbi bakoncin Majalisar mashawartan Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF), Gwamna Ortom ya ce ya kalubalanci Simon Lalong a kan maganar da yayi amma ya musanta hakan.

Rikicin Makiyaya: Lalong karya yake, na kalubalance shi a wayan tarho - Samuel Ortom

Rikicin Makiyaya: Lalong karya yake, na kalubalance shi a wayan tarho - Samuel Ortom

Yace: " An jawo hankalina akan cewa shi (Lalong) ya yi wani furuci na cewa ya gargade ni a kan kafa dokan kuma abin ya bani mamaki a ce takwara ne na jihar Flato zai fadi haka; sai na kirashi a waya kuma ya fada min bai fadi hakan ba,"

"Amma daga baya da na gani a tashar Channels Television, na yi kokarin kiransa amma bai dauki wayana ba. Na so in fada masa cewa na lallai ya yi wannan furuci."

"Kwanakin baya da na kai masa ziyara a Jos ma ce min yayi shima ya matsu ya kafa irin dokan"

KU KARANTA: Shugaban shi'a El-Zakzaky bai mutu ba, yana nan a raye - IMN

Ortom ya jaddada cewa lallai ba zai yi amai ya lashe ba a kan dokar kuma ko da Lalong ya gargade shi, ba zai saurareshi saboda mutan jihar ne suka bukaci dokan.

"Ko da ya gargade ni, abin ya fi karfi na. Wannan harkan jihar Benuwe ne ba Plateau ba,"

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel