2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

- Fayose ya ce har yanzu bai janye sha’awar neman shugabanci kasar ba

- Gwamnan ya ce ya dan ja birki ne saboda zaben gwamna da za a gudanar a jiharsa

- Fayose ya bayyana cewa zai sake yin nasara a kan Fayemi idan APC ta sake tsayar da shi

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose, a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu ya jaddada cewa bai janye daga neman takarar shugaban kasa wanda za’a yi a shekara ta 2019 ba, duk da cewa jam'iyyar PDP ta zartar da tikitin zuwa arewacin kasar.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Fayose ya ce ya dan taka birki a kan yakin neman shugabancin ne saboda zaben gwamnan jiharsa wanda za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli, 2018, inda kuma ya ce yakin neman zabe zai fara daga tushe bayan zaben jihar.

Gwamna ya kara da cewa zai sake yin nasara a kan Dokta Kayode Fayemi idan jam’iyyar APC ta sake tsayar da shi a matsayin dan takara, inda ya ce wannan ba wai barazana bane burinsa ne.

2019: Har yanzu ina kan baka na – Inji Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Fayose

KU KARANTA: Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

Da yake jawabi a yayin ganawa tare da malamai a makarantun firamare da sakandaren gwamnati a gidan gwamnati a Ado Ekiti, Fayose ya ce: "Ina nan daram a kan sha’awar takarar shugaban kasa, ina jira ne kawai a kammala zaben gwamnan jihar, bayan nan zan iya samun lokaci”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel